‘Yan Boko Haram na kashe junansu

‘Yan Boko Haram na kashe junansu

Ft-Masu goyon bayan Al-Barnawai da na Shekau na yakar Juna

-Mayaka 18 da iyalansu sun yi saranda ga sojoji

-Magoya bayan Albarnawi na zargin na  Shekau da Jihadin Karya 

‘Yan Boko Haram na kashe junansu
Barnawi ya zargi Abubakar Shekau da yin jihadin karya na kashe mutane da kwashe dukiyoyinsu

A sakamakon bayyana Al-Barnawai a matsayin sabon shugaban Kungiyar Boko Haram, ‘ya ‘yan kungiyar sun shiga yakar junansu, a inda bangarorin biyu suka hallaka da kuma jikkata da yawa daga cikinsu.

Wani mazaunin kauyen Mele Kaka ya ce, ‘yan bangaren Barnawai sun kai wani hari a kan magoya bayan bangaren Shekau a yankunansu, bayan kai harin suka fadawa mazauna kauyen cewa, magoya bayan Shekau “sun kaucewa tafarkin jihad na gaskiya”  saboda suna kisan wadanda da ba su ji ba, kuma su gani ba, suna kuma kawashe dukiyoyinu.

KU KARANTA KUMA: na da kyakkyawar alaka da ‘yan Boko Haram –Aisha Wakeel

Wani dan kungiyar Vigilante mai sintiri a Monguno, ya shaidawa wani kamfanin yada labarai ina Bloomberg  cewa, fadan da ake yi tsakanin bangarorin biyu ya tillastawa kimanin wasu ‘yan kungiyar su 18 da iyalansu mika wuya ga Sojoji a yankin.

Dan sintirin ya kuma ci gaba cewa, “wadanda suka mika wuyan na hannun sojojin da ke Monguno, kuma fadan da ake yi tsakanin bangarorin biyu ne ya tilasta musu zame jiki su miki wuya.”

KU KARANTA KUMA: Shekau ya mayar da martani ga nadin sabon shugaba

Rarrabuwan kawunan shugabannin biyu na kungiyar ta’addancin, ya faru ne a watan jiya, bayan da kungiyar ISIS ta sanar da Abu Mus’ab Al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar da ta yi mubayi’a ga a gareta a watan Maris na shekarar 2015, Abubakar Shekau ya ce har yanzu shi ne shugaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng