Wata yarinya tayi shuka a cochi da kudin makarantar ta

Wata yarinya tayi shuka a cochi da kudin makarantar ta

Sabbin al'amura na kara karuwa a rayuwa, amman ya zakayi idan har wanda ka sani yayi wannan abun?

Yawancin cochin fentakos suna kwadaitama mabiyan su dasu dunga biyan kudin kula da cochi ( kashi goma na ribar su) sannan kuma su bada iri ga Allah kamar yadda yake a bible.

Wata yarinya tayi shuka a cochi da kudin makarantar ta

Alokacin da wasu sukeyin haka batare da gumin su ya bayyana ba, wasu kuma sukanyi tafiya mai tsawo domin suga sun sami abunda zasu cika alkawarin da suka dauka na bada irin.

Wata mai amfani da Tweeter ta bayyana yadda wata 'yar uwar ta tayi amfani d kudin makarantar ta kusan naira miliyan 7 domin cika alkawarin da tayi na bada kudin iri.

Gadai abunda ta rubuta a kasa.                     'Yar uwata tayi amfani da kudin makarantar ta wanda yakai £13000, a cochi domin ta dauki alkawarin data dauka na bada kudin iri, bayan dataje cochin sai ta bada kudin duka.

Inda 'yan uwanta mamaki ya kamasu, abunda kawai ta Bari a wajanta shine kudin hayarta na wata 6 dakuma kudin alawus dinta na wata 2. Kun yarda Dani, Babanta ya kusa maida ita makarantar koyar addinin kirista na Defa.

Har mahaifiyarta taso taje cochin domin ta amso kudin amman wasu yan uwanta suka hana. Saboda haka mamanta ta sanyata a aiki domin ta nemo wadannan kudaden data bada a UK.

Saboda haka, kada a yaudareka, Allah zai amshi addu'ar ka Koda baka bada kudin shuka ba a cochin ka.                                       Nayi maka wannan alkawarin hakan, ni a karkashin cochin living testimony nake.

Me kake tunani?

Asali: Legit.ng

Online view pixel