Ciwon tamowa da sauran cututtuka na kisan IDPs a Arewa

Ciwon tamowa da sauran cututtuka na kisan IDPs a Arewa

Kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa marasa iyaka koko Doctors Without Borders ta ruwaIto cewa akwai matsananciyar ciwon tamowa a bangaren arewa maso gabas wadda keda mamayar sojoji bayan barnar da 'yan ta'addar Boko Haram tayi.

Ciwon tamowa da sauran cututtuka na kisan IDPs a Arewa

A wani rohoto data sa a shafinta na yanar gizo ranar Laraba 7 ga Satumba, mai tafiyarda aikin kingiyar a arewa maso gabas Hakim Khaldi yace, ziyarar da aka kai matsugunnin wadanda aka raba da garuruwansu na nuna mutanen na fama da ciwon tamowa da kuma sauran cututtuka.

KU KARANTA:An kama ta da akwatin gawa cike da matattun yara a mota

"Ciwon tamowa shine gagarumin aikin da muke fuskanta cikin ayyukanmu. Mun binciki yara 3,293 'yan shekara kasa da biyar muka kuma ba 513 maganin ciwon tamowa. A takaice kashi 15.1 na yara na fama da ciwon tamowa, yayin da kashi 4.2 ke fama da matsanancin ciwon tamowar. An dan sami cigaba daga zuwanmu na 13 ga Yuli lokacin da mula raba abinci mai magunguna lokacin da muka ga matsananciyar tamowa wanda ya kai kashi 15.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng