Yunwa da cututtuka sun addabi 'yan gudun Hijira
Kungiyar bayar da agaji ta likitocin kasa da kasa MSF, ta bayar da rahoton cewa, da akwai matsanancin yunwa a sansanonin ‘yan gudun hijira da ke arewa maso gabashin kasar
A rahoton da ta wallafa a shafinta na Intanet a ranar Laraba 7 ga watan Satumba, Hakim Khaldi Shugaban kula da ayyuka a yankin arewa maso gabas na kungiyar ya ce, ‘yan gudun hijira na cikin mawuyanci hali a Bama inda kungiyar ta ziyarta.
Wannan bala’i ya fi kamari a yankunan da Sojoji suka kwato daga hannun Boko Haram ne, kamar garin Bama da kungiyar ta ziyarta, a inda ta ganewa idonta halin matsanancin yunwa da yiwuwar barkewar cututtuka a tsakanin ‘yan gudun hijirar.
KU KARANTA KUMA: Yunwa ta sa ‘yan gudun hijira zama ‘yan kunar bakin wake
Rahoton Shugaban kungiyar ya kuma kara da cewa, “…Yunwa ita ce babbar matasalar da muka taras ta na addabar ‘yan sansanin da muka ziyarta. A wannan ziyarar aiki mun duba lafiyar jimlar yara 3,293 ‘yan kasa da shekaru 5 da haihuwa, mun kuma ba yara 513 magani…”
Rahoton shugaban kungiyar ya kuma cigaba da cewa, “dangane da wasu matsaloli mun lura da cewa, cutar Malaria, da cututukan da suka shafi fata, da kuma gudawa, su suka addabi ‘yan gudun hjirar. Saboda an samu karuwar sauro sakamakon shigowar damina.”
Duk da cewa da akwai karamin asibiti, a cewar Mista Khaldi, amma mutane ba sa zuwa, “da akwai karamin asibiti na Ma’aikatar Lafiya da kuma UNICEF a Bama, amma ba kowa ne ya ke zuwa ba, saboda karancin magunguna, haka ma dan asibitin-sha-ka-tafi da rundunar Sojin Sama ta bude, mutane ba sa zuwa.”
Asali: Legit.ng