Sa'a ta kare ma wasu masu buga kudin bogi a jihar Oyo

Sa'a ta kare ma wasu masu buga kudin bogi a jihar Oyo

- A ranar talatar da ta gabata ne rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta cika hannu da wasu mutane biyu dake zaune a yankin Ijokodo a birnin Ibadan

- Femi Faweya mai shekara 68 da kuma Segun Fayose mai shekara 42, saboda da zargin da ake masu na buga takardun kudin bogi.

Da yake magana da 'yan jaridu jim kadan da fadawarsa a komar 'yan sanda, Faweya wanda ya ce shi tsohon malamin makaranta firamare ne, ya shiga wananna sana'ar ne bayan da wasu mutane suka damfare shi. Inda yayi asarar naira dubu dari biyu. Kuma ya ce yana matukar bukatar kudi domin ya biyawa ya'yansa wadanda ke jami'a kudaden karatu.

Faweya ya ce suna buga takardun naira dari biyar-biyar da kuma 'yan dubu daya-daya ne da na'uarar dab'i da suka saya domin wannan muguwar sana'ar. Kuma yana yin hakan ne domin ya mayar da naira dubu dari biyun sa da aka damfare shi.

Ya kara da cewa wani mutum ne ya koya masa wannan aiki, amma a halin yanzu ya mutu kusan shekara uku da suka shude.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Oyo Mista Sam Adegbuyi wanda ya nunawa 'yan jaridu wadanan mutane, ya ce rundanar sa ta daura damarar yaki da bata gari a jihar, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng