Wani matashi yayi 'zindir' saboda N10,000
Wani matashi mai kimanin shekaru 30 ya yi tafiya tsirara cikin bainar jama'a a unguwar Kabayi dake garin Mararrabar Abuja da jihar Nassarawa saboda ya mallaki naira dubu goma da aka sa masa gasa.
Majiyarmu ta rawaito cewa lamarin ya samo asali ne a lokacin da mutumin wanda aka sakaye sunansa yake bayyanawa abokansa cewa zai iya yin komai saboda kudi. Inda har ta kai ga ya fadawa abokan nasa cewa har yawo tsirara a cikin jama'a zai iya yi saboda kudi, hakan ya sa abokan nasa suka ce idan har kuwa ya yi tafiya tsirara za su ba shi naira dubu goma.
Majiyar ta mu ta kara da cewa daga bisani mutumin ya baiwa abokan nasa mamaki, inda ya yi zigidir haihuwar uwarsa, ya soma tafiya cikin bainar jama'a da rana tsaka. Yayin da masu mamakin hakan suka yi ta binsa da kallo, wasu na gefen titin kuma musamman mata suka yi ta kau da idanuwansu.
Asali: Legit.ng