Wani mutum ya kone alokacin dayake amsa waya a kicin

Wani mutum ya kone alokacin dayake amsa waya a kicin

Sama da shekaru, anata gargadin mutane game da amsa waya a gidajen man fetur ko kuma a inda akwai gas, amman abun mamaki, ba duka mutane suke jiba, sai bayan sun shiga cikin matsala sannan zasu daina amfani da wayar a irin wuraren.

A ranar Talata 6 ga watan satumba, wata mata ta tura ma jama'a wannan hotunan domin suga abunda ya faru dan su gyara, wanda mijinta Likitane wanda yayima mutane 6 magani sanadiyar amsa waya a kicin.

Wani mutum ya kone alokacin dayake amsa waya a kicin

Ta sanya hotuna guda biyu na mutanen da suka samu matsalar kuna ta hanyar amsa waya a kicin, inda tace;

Sunana Dakta Ademola, kwana uku da suka wuce, mijina wanda shima Litikane ya sanya hotunan mutane 6 da suka kone sanadiyar amsa wayar hannu a kicin kusa da rusho mai amfani da gas, inda aka kaisu sashin masu kuna da ake cema OOUTH a asibitin dayake aiki.

Ya kara da cewa wanda mutane su daina amsa waya a gidajen mai dakuma cikin kicin din da ake amfani da gas. Ku taimaka ku tura kowa ya gani, musamman masoyan ku.

Kai.... Nasan da yawan mu munayin wannan kuskuren, saboda haka mu kiyaye!

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng