Motar shugaban kasar Rasha tayi hatsari
- Motar shugaban kasar Rasha tayi hatsari
- Jaridun kasar Rasha sun ruwaito labarin wani mummunar hatsari da ta rutsa da motar shugaban kasar Rasha Viladmir Putin, sai dai shugaban ya tsallake rijiya da baya da yake baya cikin motan
Rahotannin sun bayyana cewa hatsarin ya afku ne lokacin da wata mota kirar manrsandi tayi taho-mu-gama da motar shugaban kasar a kan titin Kutuzovsky a babban birnin Moscow ranar litinin 6 ga watan Satumba, wanda yayi snadiyyar mutuwar direban motar.
KU KARANTA: Kasar Turkiyya ta halbo jirgin yakin na Rasha
Jim kadan bayan faruwar hatsarin, sai ga masu bada agajin gaggawa sun hallara wajen, sai dai kash! Sun makara, inda direban motar Viladmir ya riga ya mutu. Inda aka garzaya da direban marsandin cikin mawuyacin hali.
Har zuwa yanzu ba’a samu cikakken bayani ba dangane da hatsarin, amma dai rahotanni sun nuna cewa direban ya kwashe shekaru 40 yana tuka mota.
Motar na da rajista a hukumance na mallakin gwamnatin tarayya. An rufe hanyar Kutuzovsky na tsawon awa daya don dauke motocin, wanda hakan ya kawo cinkoso kan hayar. Zuwa yanzu dai yansandan yankin sun fara gudanar da bincike.
Kwanan nan Legit.ng ta ruwaito an kama Vladmir a kasar Amurka sakamakon wuce gona da iri da yayi.
Asali: Legit.ng