Barci ya kwashe wani barawo a yayin da yaje sata

Barci ya kwashe wani barawo a yayin da yaje sata

Wani Fasto dake Asamankese a shiyyar gabashin kasar Ghana, mai suna Fasto Asare Nyarko yana cikin al'ajabi, bayan da wani barawo mai kimanin shekaru 27 ya shigar mashi gida kuma barci ya kwasheshi a dakinsa.

Adom a yanar gizo ya bayyana cewar, Richard Yeboah, ya fadoma Faston gidan sane ta katargan gidan, sannan ya shiga dakin sa ta silin. A zantawar da Fasto Nyarko wannan abun yace, Shida iyalin sa sunje cochi da suka dawo sai suka tarar da kofofin gidansu a bude.

Faston yace, sun lura wani ya taba daya daga cikin fitilun gidan ayayin da suka lura da yanayin fitilun dake haskaka gidan, wani bayayi saboda haka ya sanya gidan yayi duhu. Sai suka je suka kai maganar ga yan sanda, bayan da suka shiga gida da jami'an tsaro da wasu mambobin cochin sai kawai suka tarar da barawo na barci tukuru a tsirara a kan gadon faston.

Barci ya kwashe wani barawo a yayin da yaje sata

Ga dai abunda faston ke cewa " Naje cochi nida iyalina, daga dawowar mu, sai muka ankara cewa wani ya balle mana gida kuma an bincike mana dakuna. Sai nayi sauri nakai rahoto a ofishin yan sanda, sai muka dawo dan mu dauki hotunan abunda muka gani, sai kawai mukaga an balle mani daki, da muka shiga dakin sai muka tarar da barawon yana kwance yana barci yana munshari.

Har saida muka kirashi sau uku sannan ya farka, kuma muka damka shi a hannun yan sanda. A gaskiya har yanzu ina mamakin yadda akayi barawon nan baiji maganarmu a dakin ba"

Haka kuma ya gano cewar wanda ake zargin yaso ya sace masa wasu kaya amman washegari ya gansu a wajen gidan.

Fasto Nyarko yace wanda ake zargi yanzu haka yana tsare a yan sanda, alokacin da aka tambaye shi, sai yace yana neman wajan da zai huta ne bayan da yayo tafiya mai nisa tun daga Senegal.

Hmm!

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng