Sojan daya ya shirya mutuwa
Sojan daya shirya mutuwa ma Najeriya
Wani jami’in rundunar sojan Najeriya dake yaki da yan kungiyar Boko haram a arewa maso gabashin kasarnan mai suna Sabo Habu ya bayyana yanayin aikin soja a shafinsa na Facebook.
Ya ce wanda zan yi alfahari idan na mutu yayin yima kasa ta hidima, ba zan taba yin da na sanin mutuwa yayin kare kasata ba. idan janar zai shiga ruwa, ni wanene toh? Allah ya albarkanci rundunar sojan kasa, ina alfahari da kasancewa daya daga cikin mayakan rundunar sojan, Allah yayi ma Najeriya albarka.
Sojojin dake yaki da mayakan Bokoharam da tsagerun Neja Delta suna fuskantar hadarurruka da dama yayin gudanar da ayyukansu.
KU KARANTA: Sojoji sun kashe Yan Boko Haram, sun kwace makamai
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baiwa bangaren tsaro muhimmanci sosai. An zabi Buhari a matsayin shugaban kasa ne sakamakoon alkawarin da yayi wajen dawo da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas wanda rigimar Bokoharam ta dabaibaye.
Gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasara wajen karya lagon yan Bokoharam, amma har yanzu ba’a gama yakar su ba.
Asali: Legit.ng