Saura kiris a rikicin addini ya barke a Lagos

Saura kiris a rikicin addini ya barke a Lagos

By-Hausawa mazauna unguwar Ketu sun nemi hallaka wani a bisa zargin batanci

-Saura kiris a rikicin addinin ya barke a Lagos

-‘Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin da kuma tsare wanda ake zargi

Saura kiris a rikicin addini ya barke a Lagos

Wani mai shagon sayar da magani dan kabilar Igbo, ya tsallake rijiya da baya yayin da wasu fusatattun matasan Hausawa suka yi kokarin hallaka shi a bisa zargin rubuta wasu kalaman batanci.

Matumin mai suna Emmanuel Emeka ya gamu da fushin matasan ne a unguwar Ketu a jihar Lagos, bayan da ake zargin ya rubuta wata kalma da ake zargin ta sabo ce a wata mujalla, wacce hakan ta harzuka matasan Musulmin Hausawa a unguwar, a cewar jaridar Punch.

Rahoton jaridar na cewa, matasan sun yi dandazo a kofar shagon Emeka na sayar da maganinsa, a inda suke nufin kona shi, kafin ‘yan sanda su kawo dauki; rahoton jaridar ya kuma ci gaba da cewa, da zuwan ‘yan sandan matasan suka watse, wanda ba don haka ba, da ya rikide zuwa rikicin addini ganin yadda abokan Emeka suka fito aka kuma soma ba hammata iska.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Dalapo Badmos ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya kuma kara da cewa, sun tafi da Emeka ofishinsu na yankin domin kare lafiyarsa, bayan ‘yan sandan sun samu nasara tarwatsa matasan da kuma hana kona shagon.

A ‘yan kwanakin nan ana samu tashe-tashen hakula da aka danganta faruwarsu ga kalaman da Musulmai ke ganin batanci ne a addininin Islama daga Kristoci, wanda hakan ta kai ga kone wasu mutane 8 a jihar Zamfara a bisa wannan zargi a makonnin da suka wuce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng