Sari Sanusi ya maganta kan auren daya
Mai girma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu, ya bayyana cewa ba shi da kwarkwara.
Sarkin, wanda ya yi wannan bayani a wata hira da jaridar THISDAY Style ta yi da shi, ya ce yin kwakwara ra'ayi ne.
Sarki Sanusi na biyu ya kara de cewa auren mace daya bai taba zama dole ba a addinin Musulunci.
A cewarsa, "Al'ada ce kuma ya danganta da ra'ayin mutum", sannan ya kara da cewa "ina da 'yan uwa wadanda mace daya kawai suka aura kuma mahaifina bai taba zama da mace fiye da daya ba a lokaci guda, duk da cewa ya yi aure fiye da sau daya".
Tsohon gwamnan na Babban Bankin Najeriya, wanda ya shafe sama da shekaru uku a wannan matsayin, ya ce ya dade yana sha'awar ya zama Sarkin Kano.
"A wannan masarautar na tashi tun ina yaro, kuma ina da kusanci sosai da marigayi Sarki Ado Bayero. Na fahimci cewa sarauta wata kafa ce da ke ba da damar kawo sauye-sauye a cikin al'umma."
Ranar 8 ga watan Yunin 2014 ne dai aka zabi tsohon ma'aikacin bankin, wanda a wancan lokacin yake amfani da sunan Sanusi Lamido Sanusi, a matsayin sabon Sarkin Kano, kuma kashegari aka tabbatar da nadinsa a matsayin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu.
Asali: Legit.ng