Shaharren Malamin ya mutu
Isidore Okpewho,daya daga cikin manyan malaman rubuce-rubuce ya rasu.
Mutum mai lambar yabo yam utu ne yanada shekara 74. Ya kasance mai yawan rubuce-rubuce kumma edita ,wanda yayi editan litattafai 14.
Farfesa okpewho yam utu ne a wani asibiti a birnin Binghamton a birnin New York inda ya kasance yana zaune yana koyarwa tun shekarar 1991.
Ya karar da rayuwarshi cikin koyarwa. Ya koyar a jami’an New York da ke Buffalo (1974-76), Jami’ar Ibadan , (1976-90),Jami’ar Havard (1990-91),da jami’ar jihar New York a Binghamton.
KU KARANTA : Jami’in watsa shirye-shirye Olalomi ya kwanta dama
Game da cewar Nuka Otiono,mazaunin kasar Canada,tace Farfesan ya rasu ne a ranar 4 ga watan Satumba bayan rashin lafiya. Jaridar Premium Times ta bada rahoto.
Asali: Legit.ng