Wani malamin addinin kirista ya ce shi dan luwadi ne

Wani malamin addinin kirista ya ce shi dan luwadi ne

 

Bishop na garin Grantham, a Burtaniya, Nicholas Chamberlain, ya fito fili ya fadi cewa shi ɗan luwaɗi ne.

Wannan dai shi ne karon farko da wani Bishop daga cocin Ingila ya fito ƙarara ya bayyana ɗabi'arsa ta neman jinsi guda.

A bara ne dai babban limamin cocin Ingila, Archbishop na Canterbury, Justin Welby, ya nada Chamberlain a matsayin Bishop.

Justin Welby ya ce yana sane da cewa Chamberlain na da halayyar neman maza amma neman mazan ba zai shafi ayyukan coci ba.

Ya ƙara da cewa " Ya daɗe yana soyayya da 'yan luwaɗi irinsa."

Sai dai kuma Bishop Chamberlain ya ce yana bin umarnin cocin ne wadda ta ce duk wani limamin da ke neman maza, to dole ya kame daga saduwa da su.

Wasu na kallon kalama na mista Chamberlain da wadanda za su bude wa wasu limaman cocin kofa wajen bayyana bukatarsu ta 'ya'ya maza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng