Buhari ya yaba ma Zuckerberg

Buhari ya yaba ma Zuckerberg

-Shugaba Buhari ya yaba da saukin halin attajiri Zuckerberg

-Buhari ya gana da attajirin a fadar shugaban kasa a cikin sirri

-Hadimin shugaban ya bayyana sakamakon ganarwa

Buhari ya yaba ma Zuckerberg

Shugaba Buhari ya yaba da saukin halin attajiri mai dandalin Facebook, duk da cewa shi ne na bakwai a jerin masu kudin duk duniya.

A bayanin da Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan kafafen yada labarai, Femi Adesina ya lika a shafinsa na sada zumunta da muhawara na Facebook, inda ya ke bayyana abubuwan da aka tattauna a yayin ganawar, ya rawaito cewa, shugaba Buhari ya ce, halayyar matashin attajirin abin koyi ce ga ‘yan kasar.

A cewar sanarwar, shugaba Buhari ya kuma godewa shugaban Kamfanin Facebook din da samun lokacin da ya zo Najeriya, har kuma ya gana da matasan kasar, a inda suka yi musayar ra’ayi kan fasahar sadarwa mai karfafa gwiwa.

Shugaba Buhari ya kuma kara da cewa, “a al’adarmu a nan kasar, ba mu saba ganin manyan mutane attajirai kamar ka ba a cikin karamar shiga, tare da fita gudu har da share gumi a kan titi, a nan sai dai ka gansu a cikin motoci masu raba…”

KU KARANTA KUMA: Tauraron dan Adam da zai kawo cigaba Afrika ya samu matsala

A nasa jawabinsa Mark Zuckerberg ya ce, 'yan Najeriya sun burge shi da irin kwazonsu, da kokari, da kuma hazaka, musamman wadanda ya gani inda ake koyon fasahar zamani a unguwar Yaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel