Kanu yana da ciwon kai
-Tsohon dan wasar gaba Kanu Nwanko baya jin dadin matsalolin da ke faruwa a kungiyar kwallon kafa
-Kanu ya bayyana cewa abin ya dameshi kuma ya dami kowa kasancewar Najeriya taka sa zuwa gasar cin kofin nahiyar Africa
Kanu wanda tsohon kaftin din super Eagle ne yace matsalolin da kungiyar Super Eagle ke fuskanta basa bari yayi bacci mai dadi
Yace abinda yafi damunshi, kuma ya dami kowa shine kasa zuwan kungiyar ta Najeriya zuwa gasar cin kofin nahiyar Africa, gashi kuma ko kana nan kungiyoyin na (U-17 da U-20) suma basa wani kokari.
Kanu wanda mutane ke kira papilo yace" wallahi kullum abun da nake tunani kenan, kuma kullum abun na damuna , be kamata ace kungiya kamar Najeriya abubuwan nan ke faruwa da su.
Abin da zance shine mu hada kanmu, mu bada goyon baya dan farfado da kungiyar, saboda ba lalle kowa ya zama mai horarwa ba. Duk da cewa baya nufin komai koda kungiyar Najeriya zata doke Tanzania a wasar da zasu doka gobe, amma Kanu yace ze zama babban gwaji ga sabon mai horarwa Gernot Rohr.
Amma nasan cewa dayawa magoya bayan kungiyar Najeriya zasu so suga yanda sabon kocin ze doka wasa da kuma yanda ze zabi yan wasa, duk da kungiyar ta samu matsaloli amma zamu hadu mu gyara.
Asali: Legit.ng