Matan aure na karuwanci domin ciyarda iyalansu-Egberongbe

Matan aure na karuwanci domin ciyarda iyalansu-Egberongbe

 

-Shugaba Muhammadu Buhari na shan suka daliln halin da kasar ke ciki bayan bayanin cewa kasar ta shiga koma bayan tattalin arziki

-'Yan Najeriya da yawa na kuka da matsin tattalin arzikkn kasar

-Bayanin ya fito ranar Laraba 31 ga Agusta 2016, daga hukumar kididdiga ta kasa mallakin gwamnati

-Wani jigon APC, Mufutau Egberongbe, yace al'amurran kasar sun kara rincabewa

Matan aure na karuwanci domin ciyarda iyalansu-Egberongbe
karuwai

 

Labarai na bazuwa na shigar tattalin arzikin Najeriya cikin matsatsi yayin da kasuwanci ke ja baya. A harkar sufuri  jiragen sama, kampanoni biyu, First Nation da Aerocontractors sun dakatar da zurga-zurgarsu. A wannan hirar da mukayi da Eromosele Ebhomele, Honourable Mufutau Egberongbe, wanda shine mai baiwa kakakin majalisar jihar Lagos Mudashiru Obasa, kan harkokin ayyukan majalisa, yana gaya ma shugaba Muhammadu Buhari yanda zai shawo kan matsalolin tattalin arzikin kasar.

'Yan Najeriya da yawa na kukan matsin tattalin arzikin kasar. 'Yan kwanakin nan zaka ji an kama mutane domin satar kayan abinci. Wannan ba sheda bace cewa kasar ta kusa tsayawa ba?

Abin da kake gani alama ce kasar na kan hanyar durkushewa daga matsatsin tattalin arziki. Ba wai ana maganar talauci bane, a'a ana maganar matsanancin talauci a cikin kasa. Irin wannan halin ke kawo fasikanci, satar mutane, karuwanci da kananan sace sace duk don a sami abinci. Abin ya shafi matan aure wadanda ke yin duk abinda zasu iya domin rayuwa. Wannan bashi da alfanu ga kasa.

KU KARANTA : Duniya jama’a: Wata ta jefa jaririnta cikin salga

Albashin da ake biyan ma'aikata da wuya yake kaisu tashar mota balle ayi maganar kaiwa gida. An dade a haka, amma yanzu abin ya kazance. Abinda naira zata iya saye shine yafi damun kowa, abin sai tabarbarewa yake ba alamun gyaruwa. Ga kasar da komi sai an shigo dashi kamar tamu, komi sai ya tsaya cik domin ba zaka iya yin wani shirin kasuwanci ba hayin da kudin canji suke da wuya. Abin yana da ban damuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel