An kama wani mutum da wandon mace jike da jini a jahar Ribas

An kama wani mutum da wandon mace jike da jini a jahar Ribas

An kama wani mutum da ake zargi a jahar Ribas ranar Laraba 31 ga watan Agusta.

Acewar Oladele Oyelude wanda shiya bayyana abun a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewar an kama mutumin ne da wandon mace jike da jini a hawan da jami'an tsaro ke binciken ababan sufuri a hanyar Emohua a Degema Axis a jahar Ribas.

Mutumin dai ya dauko dan Achaba daga Buguma zaije Degema inda ya biyo ta mahadar Obakri, alokacin da dan achaban wanda ya dade yana sauraron irin wayar da mutumin yakeyi tun sadda ya dauko shi. Domin kuwa yana ta faman kiran waya kuma shima ana kiran sa, wanda wayar yake nuna alamar mutumin baida gaskiya akan hanyar su na tafiya.

Inda dan achaban ya tsaya inda jami'ai suke binciken ababan hawa, yaje ya gayama jami'an tsaro dan gane da mutumin.

Inda hukumomin tsaro suka amshi jakar ledar dake hannun sa, suka duba, wanda anan ne sukaga wandon mace jike da jini tare da wasu kayayyaki na Sawa suma jike da jini duk a cikin su jakar ledar.

Inda suka fara tambayarsa, inda yaki bada gamshashiyar bayani da hankali zai dauka dangane da inda ya samu kayan.

Haka kuma, sun fahimci cewar yanata dabir-dabir dangane da irin amsoshin da yake bayarwa.

Daganan kuma suka kamashi suka sa masa mari.                                                         Hmnnn, abin mamaki, kalli hotuna.

An kama wani mutum da wandon mace jike da jini a jahar Ribas
An kama wani mutum da wandon mace jike da jini a jahar Ribas
An kama wani mutum da wandon mace jike da jini a jahar Ribas

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng