Mai facebook yaci abincin gargajiya
Mamalakkin kamfanin sadarwa ta facebook kuma na 7 cikin jerin masu kudin duniya Mark Zuckerberg ya sauka kasar Kenya don ganawa da kananan yan kasuwa.
Saukarsa kasan keda wuya aka hange shi yana cin abinci irin na kasar tare da abokinsa Joseph Mucheru sakataren watsa labarai na kasar, Zuckerberg yaci tuwon Ugali da kifi.
A jiya 1 ga watan satumba ne Zuckerberg ya sauka kasar Kenya inda ya fara kai ziyara kamfanin sarrafa na’ura mai kwakwalwa iHub.
Zuckerberg ya bayyana ganawarsa da Joseph Mucheru ta shafinsa na facebook yana cewa “na ci abincin rana tare da Joseph Mucheru sakataren watsa labarai na Kenya, mun tattauna batun samar da yanar gizo a kasar Kenya. Mun ci abinci a gidan cin abinci na MAMA OLIECH, daya daga cikin abin da nafi so idan nayi tafiya shi ne in ci abincin kasar, naji dadin tuwon Ugali tare da katon kifin.”
Asali: Legit.ng