Yar shekaru takammala karatun lauya
Komai mai yiwuwa ne a rayurwar nan, kada ka sake wani kalubale ya hana ka cigaba, idan ka samu wata dama, toh kayi amfani da damar ka.
Mutane da dama sun gaza yin amfan da damansu na samun nasara a rayuwa sakamakon irin mataki da shwarwari da suka daukan ma kansu, wasu kuma sukan natsu kuma su gyara mtsalolinsu.
Daya daga cikin matsalolin da mutane suke fuskanta shine yawan son kai; sun gwammace suyi ta kushe al’amuran wasu. Idan ka sake ka bari wasu ne ke baka ra’ayin da kake bi, toh tabbas kayi kuka da kanka.
Wata mata mai shekaru 60 Safiyo Jama Gyare ta kammala karatun digiri daga jami’ar jihar Puntland dake a can kasar Somalia. Da wannan ne ta kafa tarihin kasancewa daliba mafi yawan shekaru data kammala wannan makaranta. Safiyo ta karanci fannin sharia da doka ne don ta samu daman taimaka ma mata da wadanda ake yi ma fyade.
Safiyo tayi makukar bakin ciki cin zalin mata da ake yi, sa’nnan matsalar mutuwar aure ma na daya daga cikin abinda ke damunta musamman yadda maza ke hana matansu komai, tayi kokarin gano gaskiyar lamarin, inda ta fahimci cutan mata ake yi.
Akwai tsoffin mutane da dama cikin wannan al’umma dake komawa makaranta don cimma burinsu. Bai kamata wani ya bari shekarunsa su zame masa kalubale ba wajen cimma burinsa.
Asali: Legit.ng