Abin mamaki na farƙo da masu kimiyya

Abin mamaki na farƙo da masu kimiyya

Mafi yawanci anfi samun yan biyu masu kama daya a jinsin mutane, sai kuma gashi an samu yan biyu a jinsin karnuka masu kama daya inji masanan kimiyya, sunce sun gano yan biyun masu kama dayan na farko a bincikensu a duniya.

Abin mamaki na farƙo da masu kimiyya

Wannan al'amari dai ya faru ne a kasar Afirika ta kudu. Kuma yawancin jariran karnukan suna da abu iri daya daga 2 zuwa 12 a wasu lokutan, amman dukannin su suna da Kwai daban-daban ne kuma suna da banbanci.

Haka kuma, wadannan yan biyun an haifesu ne daga kwai daya.                           Gadai abunda masanar kimiyar suka fadi.

Iya tsawon binciken mu na tsawon lokuta, wannan shine nasaran da muka samu na farko sakamakon samun nasarar gano yan biyun karnuka masu kama daya da mukayi ta hanyar gwaji da muka gudanar ta amfani da DNA.

Abin mamaki na farƙo da masu kimiyya

Haka kuma dukkan jikinsu da sinadaren jikinsu iri dayane. Kuma kalarsu daya ne, kamar yadda ake samu a jinsin kalar yan biyun dan Adam. Wanda akafi sani yake faruwa a mafi yawancin jinsin dan Adam da kuma manyan dabbobi wato su haifi yan biyu masu kama daya a duniya.

Haka kuma wadannan karnukan su kadai ne masu kama iri daya, kuma mamansu ta kasa haifar su da kanta, wanda saida akafi amfani da sabuwar dabara ta zamani ta hanyar kyankyasar kwan su na na'uran da ke taimakawa wajen kyankyasar kwayayen karnuka, inda ananne suka auna karnukan kuma suka tabbatar da hakan, wanda mawuyacin abune a samu irin haka a jinsin karnuka.

Bazamu iya tabbatar da hakan ba ta hanyar kallonsu, amman saita hanyar gwada jinin su, wanda mukayi amfani da hanyar DNA inda suka gano cewar jinin su iri dayane.

Akwai dai rade-radi dangane da yan biyun karnuka dake yawo ada can baya, amman saidai yanzu munyi sa'a wajen tabbatar da gano jinsin na karnuka, inda muka samu sa'ar gano yan biyun masu kama daya na farko.

Wadannan jariran karnukan kamarsu daya!

Asali: Legit.ng

Online view pixel