Darussan rayuwa daga Mark mai Facebook

Darussan rayuwa daga Mark mai Facebook

Daya daga cikin abubuwan da ke burge mutane dangane da Mark Zuckerberg mai kamfanin Facebook, kuma daya daga cikin attajiran da suka fi kowa kudi a duniya, shi ne yadda ya ke tafi da rayuwarsa dangane da lafiya da kuma zamantakewa, ga kadan daga cikin su

Darussan rayuwa daga Mark mai Facebook
Mark Zuckerberg mai Dandalin Facebook ya kawo ziyara jihar Lagos a Nigeria a cikin makon nan.

Motsa jiki

Ga wasu motsa jiki wahala ne, amma ga Mark wannan wajibi ne domin kasancewa cikin koshin lafiyar da za ta ba shi damar kula dandalin Facebook mai farin jini, don haka ya ke fita motsa jiki a kullum da sanyin safiya. Mark ya na gudun nisan mil daya a kowacce rana, hakan kuwa na rage kiba, da teba, ya kuma inganta kewayawar jinin a jikin bil adama.

Abinci mai gina jiki

Attajirin ba ya cin nama, saboda da gudun kitse, Mark Zuckerberg yana sha’awar noma da cin ganyayyaki

Sadaka

Duk da cewa attajirin bai bayyana addinin da ya ke bi sau da kafa ba, amma ya yi amanna da cewa, taimakawa al’umma na kawo karin farin ciki, da walwala, wadanda za su taimaka ka samu karin lafiya. Don haka ne ya ke amfani da dukiyarsa wajen taimakawa al’ummar duniya ta hanyoyi da yawa. Bincike ya nuna cewa sadaka na kara tsawon rai da kuma kawar da hawan jini.

Kula da dabba

Mista Mark ya na da dabbar da ya ke kiwo ta nishadi, wacce a cewarsa, ta na kara masa karfin gwiwa da kuma dada kallon  rayuwar ta wata fuska.

Karatu

Saboda sabunta al’amuran rayuwa, attajirin na karanta littafi guda a kowanne mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel