Shekau ya mutu – Rundunar sojin Najeriya

Shekau ya mutu – Rundunar sojin Najeriya

– Kwamandan operation lafiya dole, Janar Lucky Irabor, ya ce shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya mutu

– Ya ce ainihin mutumin da ake kira shekau ya mutu

– Majo janar din yace soji basu magana akan abinda basuda tabbaci akai

Shekau ya mutu – Rundunar sojin Najeriya
sojojin najeriya

Rundunar sojin kasan Najeriya sun sake alanta cewa sun kashe shugaban bok haram Abubakr Shekau. Kana, kwamandan rundunar operation lafiya dole Janar Lucky Irabor ne ya sanar a wannan karo. Ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai jihar Adamawa a ranan 1 ga watan satumba. Ya ce an kashe ainihin shekau.

Yace : “Zan iya tabbatar muku da cewa an kashe ainihin shekau, na biyun ma an kashr shi, kuma mutumin da yake cewa shine shekau ma , ina tabbatar muku da cewa kwanakin baya ya raunana. Har yanzu dai bamu tabbatar da cewa ya mutu ba .

Game da cewar Janar Irabor, soji basu magana idan basuda tabbaci. Yace rundunar soin Najeriya da ke fafatawa a yankin arewa maso gabas, zasu cigaba da kai farmaki har sai sun tabbatar da cewa dan ta'adda daya bai rage ba, saboda akwai rabuwan kai tsakanin yan kungiyan boko haram din. Ya kara da cewa : “Suna sakin bidiyoyi domin nuna cewa suna nan , amma kawai barazana ce.

Tun shekarar 2009, rundunar sojin najeriya sun ta ikirarin kashe shekau, amma bai gushe ba yana sake bayyana. Shekau ya zama shugaban boko haram ne bayan kisan wanda ya kafa Boko haram , Muhammad Yusuf, a gaban jama'a. Karkashin shugabancin sa, boko haram ta kashe dubunnin rayuka kums ta kori miliyan 2 daga muhallin su. Kwanan nan, an samu rahoton cewa An yi mumunan raunana shi a ranan talata, 23 ga watan agusta.

KU KARANTA : Jini da jini : Murmushin Kada da hawayen kada

Kakakin rundunar sojin kasa, Kanal sani usman kukasheka ya ce: “Kwamandojin boko haram din da aka kashe sun kunshi Abubakar Mubi, Malam Nuhu da Malam Hamman, da sauran su. Kuma an raunans shekau a kafadar sa , da yawa dai sun raunana."

Asali: Legit.ng

Online view pixel