Wani mutum ya rataye kansa bayan wasika ga Buhari
Wani mutum mai shekaru 50 mai suna Chief Ekanem Edet dan garin Mbiabong Itam a karamar hukumar Itu a jihar akwa ibom ya kashe kansa a jiya, 1 ga watan Satumba, ta hanyar rataye kansa a cikin daki.
Amma kafin mutuwarsa, Edet ya bar wani sako ga shugaba Muhammadu buhari, vanguard ta bada rahoto. An samu cewa Edet ya rigaya da mutuwa awowi kafin aka ga wasikar.
KU KARANTA: An damke Fasto mai fyade wa yara 30
Duk da cewan har yanzu ba'a san abinda wasikat ta kunsa ba a lokacin rubuta labarin, majiya tace ya rubuta ne ga shugaba buhari.
Matarsa da yaransa biyu sun fita daga gida da safe ba tare da sanin ya rataye kansa ba. Shine tsohon sakataren majalisan kauyen Mbiabong kuma ya shahara da suna ‘Jolly Boy.’
Asali: Legit.ng