Tauraron dan Adam da zai kawo cigaba Afrika ya samu matsala

Tauraron dan Adam da zai kawo cigaba Afrika ya samu matsala

– Wanda ya kafa Facebook,Mark Zuckerberg ,wanda a yanzu haka yana kasar Kenya bayan ziyarar kwana biyun da ya kawo Najeriya inda ya hadu matasa kuma yayi ma najeriya alkawura

– Daya daga cikin alkawuran da yayi shine zai kaddamar da tauraron dan adam ga nahiyar Afrika , amma ta samu koma baya

Tauraron dan Adam da zai kawo cigaba Afrika ya samu matsala
Facebook CEO, Mark Zuckerberg a najeriya

Wannan shirin da Facebook ke yi na kaddamar da sabuwat tauraron dan adam domin baiwa yam nahiyar afrika ta samu matsala. Mark Zuckerberg ya bayyana hakan ne a ranan alhamis ,1 ga watan satumba. Ta shafin sa ta twita

Yace : “Yanzu da nike afrika, naji bacin ran samun labarin cewa tauraron SpaceX’s da zata baiwa matasa daman samun kudi a nahiyar afrika ta samu matsala.”

Amma ya nuna cewan akwai mafitan duk da matsalan da aka samu, za'a samu hanyar da zai baiwa yan najeriya yanar gizo.

“Amma mun samar wasu fasaha kamar Aquilla wacce za'a iya amfani da shi. Muna zange dantse akan niyar mu na sada zumunta, kuma zamu tabbatar da cewa kowa ya samu daman da amfanin tauraron dan Adam. Yace

KU KARANTA : Ina alfahari da harshen hausa- wanda ya kafa Facebook, Zuckerberg (Hotuna)

Wasu kafafen yada labarai kamar WPEC CBS12 News da Just News, sun tabbatar da faruwan a shafin su na twita.Mark Zuckerberg ,wanda a yanzu haka yana kasar Kenya bayan ziyarar kwana biyun da ya kawo najeriya. Kana yayi alkawarin cewa Facebook zata kara wasu kabilolin najeriya.

 

 

 

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng