Rundunar Sojin sama na ma Boko Haram lugudan wuta

Rundunar Sojin sama na ma Boko Haram lugudan wuta

– Rundunar Sojin sama Najeriya sun kai farmaki sansanin da shugabannin boko haram da aka raunana ke yin jinya.

– Yan tada kayar bayan sun koma sansanin ne bayan harin da aka kai musu a ranan 20 ga watan Augusta,wanda yayi sanadiyar mutuwan akalla su 300.

– Rundunar sojin dai har ila yau batada takamamman Wadanda aka kashe, bidiyon harin da suka kai ya nuna cewa anyi musu barna sosai

Rundunar Sojin sama na ma Boko Haram lugudan wuta
Soldiers

Rundunar Sojojin sama Najeriya sun kai farmaki sansanin da shugabannin boko haram da aka raunana ke yin jinya a Tumbin Rego ,Jihar Barno.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta wata jawabin da ta saki a ranan alhamis, 1 ga watan Satumba , ta kai harin je ranan 29 ga watan Agusta.

Tace ta samu labarin lekan asiri cewa akwai kwamandojin boko haram Wadanda suka tsira a harin da aka kai tanan 29 ga watan agusta amma sun raunana, suna jinya a wata sansani da ke Tumbun rego.

Bayan samun rahoton, sojin saman ta kai wa sansanin mumunan farmaki. Duk da cewan har yanzu ba'a san yawan wadanda aka kashe ba, Amma bidiyon ya nuna cewa an samu nasara saboda wutan da ke tashi a wurin.

KU KARANTA : Jami’in soja ya bayyana sirrin Boko Haram

A bangare guda, rundunar sojin kasan Najeriya sin sake alanta mutuwar shugaban boko haram, Abubakr Shekau. Amma, wannan karo, kwamandan operation lafiya dole, Janar Lucky Irabor ne ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai jihar Adamawa a ranan 1ga watan satumba. Ya ce an kashe ainihin shekau.

 

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel