Dan wasan Nollywood ya warke daga ciwon mutuwan barin jiki
- Wani sanannen jarumi dan wasan Nollywood, Ernest Asuzu, wanda yayi fama da ciwon mutuwar barin jiki na tsawon lokaci
- A yanzu kuma wani Faston Jeremiah Omoto Fufeyin na Crist Meryland Deliverance Ministry a Warri jahar Delta, ya warkar dashi, haka kuma ya bashi kyautar sabuwar Mota mai tsada dakuma kudi
Jarumin wanda yasha samun kyaututuka a Nollywood kafin ya samu matsalar shanye rabin jiki a shekarar bara, amman sai gashi a shekarar 2016, ta kasance shekarar da yayi sa'a a rayuwar sa, alokacin da wani mutumin Allah yazo ya taimake shi.
Yanzu haka Ernest Asuzus, ya dawo da sabuwar rayuwar sa kamar da. A lokacin daya shafe shekara guda a mercyland, Asuzu ya samu lafiya sosai akan rashin lafiyar dake damunsa. Wanda yanzu haka yana zuwa ko ina.
Babban Faston yaba jarumin kyautar sabuwar Mota kirar jeep wanda kudinta yakai miliyan 3.5, sannan kuma ya bashi kudi har naira miliyan 1.5 domin ya fara sabuwar rayuwa mai inganci.
Nagode Allah da sabuwar rayuwa!
Asali: Legit.ng