Majalisan dattawa na alanta neman ma’aikata

Majalisan dattawa na alanta neman ma’aikata

- Majalisan dattawan Najeriya ta alanta talar neman ma’aikatan bidiyo guda biyu domin gidan talabijin din da ta ke shirin budewa

- Majalisan dattawa ta bayyana hakan ne ta kafar sada zumuntar ta ta Twitter

- Za’a fara nema ne daga ranar 5 ga watan Satumba

Majalisan dattawa na alanta neman ma’aikata

Suka ce: “Muna neman editocin bidiyo guda biyu domin aiki a gidan talabijin majalisa. Idan kana da bukata? Zamu fara dauka ranar 5 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya amince a ciwo bashi daga kasashen waje

Amma, shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa majalisar fa bata da kudi a yanzu. Ya fadi hakan ne a ranar talata,24 ga watan agusta. Ndume yace majalisar tarayyan na fuskanta matsala wajen sufurin kudi. Yace yan majalisan basu samun Albashi a lokacin da ya kamata kuma hakan na shafan yan siyasan.

Amma yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu akan neman ma’aikatan. Da dama sun nuna bacin ran su , wani yace: “menene amfanin tallatawa tunda yan uwanku zaku dauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel