Gano sinadarin Nickel zai habaka ci gaba a ma'aikata

Gano sinadarin Nickel zai habaka ci gaba a ma'aikata

- Ana sa rai gano sinadarin Nickel zai taimaka fadada tattalin arzikin Najeriya

- Ana bayyana kyaun sinadarin cikin mafi kyawu a duniya

- An sake ma ma'aikatar ma'adinai suna da karin girma.

Gano sinadarin Nickel zai habaka ci gaba a ma'aikata

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta bada Izinin sakema ma'aikatar albarkatun kasa suna dalilin gano  wani sinadari maras yawa a duniya mai suna nickel a arewacin kasar. NAN ta ruwIto Kayode Fayemi na fadar haka bayan taron majalisar zartaswa wanda shugaba Buhari ya jagoranta. Yace daga yanzu sunanta ma'aikatar albarkatun kasa da sarrafa karafa

Fayemi ya bayyana sabon salon da zai habaka gudummuwar da ma'adinai zasu bada wajen arzikin kasa wanda yazo dai dai da kokarin Buhari na fadada tattalin arziki. Ya ci gaba da cewa a sabon salon za'a kirkiro hukumar sa ido mai zaman kanta a masana'antun sarrafa sinadarai wadda masu hudda da sinadarai ke bukatar a kafa. Ya kara da cewa:

"Inda wannan sabon salon yasha bam-bam, kuma dori ne bisa ga na 2012 wanda majalisar zartaswa ta amince dashi shine jajircewarmu wajen kafa hukuma mai zaman kanta wadda zatasa Ido kuma wadda masu saka jari suka bukata yadda ma'aikata bazata zama mai kula da harkokin ma'adinan ba".

KU KARANTA: Karkar Nigeria ta yanke saka da samun ma’adinai a Kaduna

Shi dai sinadarin wanda wani kwararre kuma masanin harkokin ma'adinai dan kasar Australia ya gano a garin Dangoma a jihar kaduna ana bayyana shi kamar haka:

"Kwallayen sinadarin wadanda ake cewa na kunshe da kashi 90 na nickel ana daukarsu tamkar na farko da aka fara gani a duniya a yadda suke baje ko Ina kuma zasu yi saurin kawo kudi domin ba za'a kashe kudi da yawa ba wajen hako shi da nazartarshi,  abinda ke ba masu bincikensa sha'awa."

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng