Ohaneze na gargadin IPOB kan cin dunu

Ohaneze na gargadin IPOB kan cin dunu

- Matasan Ohaneze sun ce basu da hannu cikin rikice rikicen IPOB

- Suna gargadin 'yan rajin Biafra su daina cin dununsu

- Gungun 'yan Biafran na cikin rudani dalilin rabuwa gida biyu

Kungiyar matasan Ohaneze koko Ohaneze Youth Council (OYC) ta nisanta kanta daga matsalolin dake damun kungiyar 'yan rajin Biafra ko Indigenous People Of Biafra (IPOB) wadanda suka jaza rabuwar kungiyar gida biyu.

Ohaneze na gargadin IPOB kan cin dunu

Wani gungu mai kiran kansa gyararrun 'yan rajin Biafra koko Reformed Indigenous People Of Biafra (TRIPOB) ya balle daga IPOB wanda yace ya daina gwagwarmayar neman 'yancin kasar Biafra, mamadin haka suna bukatar ganin ana damawa da Igbo a Najeriya. Ana cewa Ohaneze nada hannu wajen kirkirowar sabon gungun amma Vanguard ta ruwaito OYC na cewa ba hannun kungiyar ko shugabanta Mazi Okechukwu Isiguzoro cikin rikice rikicen kungiyar 'yan Biafran.

KU KARANTA: Laifukan Jonathan da Tampolo a yankin Niger Delta

"Wannan karya ce karara. Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo a duk duniya baki daya bata da wata alaka da TRIPOB kuma bata da hannu cikin rigingimun dake addabar IPOB. Mun yima wani wai shi Elliot Uko tare da mai magana da yawun IPOB Clifford Iroanya gargadi da su daina cin dunun shuwagabannin matasan Ohanaeze Ndigbo ko kuma mu dauke su tamkar abokan gaban Igbo.

Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo a duniya baki daya itace babbar kungiyar matasan Igbo kuma bata goyon bayan kirkiro Biafra kuma bata goyon bayan shugaba Buhari a ranar 1 ga Oktoba 2016, amma tana goyon bayan sakin duk 'yan Biafra dake tsare.

"Mun amince a sake fasalin kasar kamar yadda taron kasa da akayi cikin 2014 ya zartas kuma muna kiran shugaba Buhari da ya duba. Muna ba IPOB shawara su daina tsoma kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo cikin parpagandarsu" cewar Mazi Okemiri Alex a wata takarda daya sama hannu, a matsayin shugaban shuwagabannin Kungiyar matasan Ohanaeze Ndigbo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng