Jiragen Aero za su daina tashi a Najeriya

Jiragen Aero za su daina tashi a Najeriya

Jirgin kasuwanci mafi girma na biyu a Nigeria Aero Contractors ya bayyana cewa zai dakatar da sufuri daga farkon watan Satumba.

A cikin wata sanarwa kamfanin na Aero ya ce faduwar darajar Naira da aka ringa fuskanta a cikin watanni shida da suka gabata ya sa kamfanin ba ya iya cin riba.

Kamfanin dai yana da ma'aikata sama da 1,000. Shekaru biyar da suka wuce kamfanin na da jirage 18 da kuma jirage masu saukar ungulu da dama. Toh! Amma daga watan Yulin bana, jiragen kamfanin sun ragu zuwa biyu.

Aero Contractors shi ne kamfanin sufurin jiragen sama na uku da ya dakatar da zurga-zurga a Najeriya saboda matsalar tattalin arziki.

Kasar dai na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi girma a cikin shekaru goma, sakamakon faduwar farashin man fetur, da kuma hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa kan bututan mai a yankin Niger Delta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng