Buhari ya amince a ciwo bashi daga kasashen waje

Buhari ya amince a ciwo bashi daga kasashen waje

- A wani yunkuri na farfado da tattalin arzikin Nijeriya

- Shugaba Buhari ya amince a karbo basussuka daga cibiyoyin ba da lamuni na kasashen waje da nufin aiwatar da manyan ayyukan raya kasa musamman wutar lantarki.

Da take karin haske game da batun, Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta ce za a karbo basussukan daga cibiyoyi masu saukin ruwa da suka hada da Bankin Duniya, Bankin Ci gaban Afrika, Bankin Exim na China, sai kuma Hukumar ba da lamuni ta Japan. Ta ce gwamnati za ta mika wannan bukata ga majalisar dokoki don amincewarsu.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a jiya ne wasu alkaluma da Hukumar Kididdiga ta Najeriya wato National Bureau of Statistics (NBS), ta fitar sun nuna cewa kasar ta samu koma-baya a tattalin arzikinta.

Alkaluman da hukumar ta sakisun nuna an samu tawayar kaso biyu cikin dari na arzikin kasar da mutanenta, a watanni ukun da suka gabata.

Hakan dai na nuni da cewa, Najeriya ta fada cikin kangin tattalin arzikin da ya fi kowanne a tsawon shekara goma. Da man ko a watanni ukun farko na bana, tattalin arzikin ya samu komada da kaso 1.70 ne kawai.

Hukumar ta Kididdiga dai ta ce kasar ta samu tawayar arziki da kaso 2.35.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng