Maganan Kemi Adeosun shirme ne - PDP

Maganan Kemi Adeosun shirme ne - PDP

– Jam’iyyar PDP ta siffanta jawabin ministan Kudi, Kemi Adeosun a matsayin shirme

– PDP ta ce sabanin maganan ta durkushewan tattalin arziki matsala ne ga miliyoyin yan Najeriya

Maganan Kemi Adeosun shirme ne - PDP
Kemi Adeosun,

Jam’iyyar adawar Najeriya, PDP ta sifanta maganan ministan kudi Kemi Adeosun a matsayin miyau abin tofarwa

A wata jawabin mai bada rahoton mu ya samo PDP tace durkushewan tattalin arzikin ba kawai Magana bane, abin damuw ne ga miliyoyin yan najeriya wadanda suke cikin halin kakanikaye na ci da sha da kuma gudanar da rayuwan yau d kullun.

KU KARANTA: An tsige shugabar kasar Brazil Dilam Rouseff

“Abin tsoro ne maganan da tayi a ranar da cibiyar lissafin najeriya a ta saki na cewa mutanen 4,580,602 sun rasa ayyukan su tun 29 ga watan Mayun 2015.

“Magananta ya sabawa gaskiyar hauhawar kayan masarufi,iyaye na cire yaransu daga makarantu saboda tashin kudin makaranta, tashin kudin tasarrufi, kudin haya da kuma wasu abubuwa nay au ya kullun.

“Maganan ta zagi ne gay an najeriyan da ke cikin rayuwan kunci saboda rashin iya aikinta da kuma gwamnatin Shugaba Buhari. Muna kira ga Mrs. Adeosun ta lashe amanta kuma ta daina magana kaman mai lallashi, ta fara magana kaman ministan kudi. A jawaban da zamu saki nan gaba, zamu bayyana yadda maganganunta akan kudi shirme ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel