An damke Vladimir Putin a kasar Amurka
– An damke wani mai suna Vladimir Putin a jihar Florida, Amurka
– Ana gurfanar da shi da laifi wuce gona da iri
Wata labari ke fitowa daga west palm beach a Florida yayinda wani mutum dan shekara 48 ya shiga hannun yan sanda saboda laifin da yayi. Vladimir Putin haka kawai ya fara fada da masu shaguna a yankin.
KU KARANTA: Fulani makiyaya sun kai hari ga Fayose kan dokar kiwon dabbobi
Ya fara yima ma'aikatan ihu ,kana lokacin da manajoji suka ce masa ya daina ya bar musu waje, ya kiya har sai da jami'an yan sanda suka zo.
Mr. Putin ya shiga hannun yansanda da laifin wuce gona da iri da kuma kin yarda da akama shi ta yin fada da jami'an tsaro. Ya gurfana a kotu wannan mako Amma an dakatad da karar zuwa watan satumba.
Game da kafafan labarai, wannan abu ya faru a publix supermarket a makon da ya gabata.
Asali: Legit.ng