Masu zanga zanga sun kona majalisar dattijan Gabon

Masu zanga zanga sun kona majalisar dattijan Gabon

Wasu al’ummar kasar Gabon da suka gudanar da zanga zangar nuna bacin rai da gwamnatin kasar sun banka wuta a majalisar dattijan kasar.

Masu zanga zangar suna nuna bacin ransu ne da sake lashe zabe da shugaban kasar Ali Bongo yayi a karo na biyu.

Masu zanga zanga sun kona majalisar dattijan Gabon

Jima kadan da fara zanga zangar ne sai hotunan suka fara bayyana na majalisar cikin wuta, zuwa yanzu dai kamfanunuwan jaridu masu wakilai a kasar sun tabbatar da faruwar lamarin. Kamfanin BBC ta ruwaito sojojin kasar Gabon sun janye daga harabar majalisar da aka kona.

Al’ummar kasar Gabon sun fara gudanar da zanga zangar ne bayan an sanar da Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Gabon inda ya kada shugaban adawa Jean Ping.

Kamar yadda sakamakon zaben suka nuna a ranar laraba, Ali ya lashe kashe 49 na kuri’un da aka jefa, inda Ping ya lashe kasha 48.23

Masu zanga zanga sun kona majalisar dattijan Gabon

Sai dai shugaban adawa Jean Ping ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar lahadi, kuma ya dage kan bakarsa na cewa anyi magudi a zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng