Ban rubuta takardar aje aiki ba - Siasia

Ban rubuta takardar aje aiki ba - Siasia

- Siasia yace be aje matsayin shi ba a matsayin mai horar da U-23 ,amma na'aje ne bayan kwantaragi na ya kare                                                         

- Siasia yace dole NFF su biyashi duk abinda yake binsu

- Dalung ya fada ma NFF su tabbata sun biya Siasia hakkokan shi na wata 5

Sabanin rohoton da muka samu cewa Siasia ya aje aikin horar da yan kasa da shekara 23, Samson Siasia ya bayyana cewa ba aje matsayin shi yayi ba, ya dena ne saboda kwantaragin shi ya kare bayan kammala wasar Olympic.

Yayin da yake magana da jaridar Punch, Siasia yace wannan ba shine hakikanin aje aiki ba, kwantaragi na ne ze kare a karshen wasar Olympic kamar yadda yake a tsare. Dan haka kwantaragi na ne ya kare.

Sai dai, tsohon mai horarwar na yan kasa da shekara 23 ya nemi hukumar kwallon kafa ta Najeriya wato NFF da ta biya shi duk hakkokan shi da ya ke bi.

Yace wanda abinda yake da amfani anan shine, a biyani duk abinda nake bi. Ina bikatar kudin fiye da zaton ku, kuma ina da yakinin cewa nayi juriya kuma nayi kokari.

Lokacin da yake mai da martani kan rohoton aje aiki da da aka ce yayi, Siasia wanda yaci kyautar Tagulla a gasar Rio Olympic, yace yayi magana da wanda yayi rohoton amma kudin shi kawai yake so. Yace" Nayi magana da mai rohoton amma ina tsammanin wanda ake magana a kanshi an cire shi ,yayin tambayoyin, nasa wani ne, abinda aka tambaye ni shine labarin duk abinda ya faru a Olympic, wanda ya hada har da zaman mu a Atlanta.

Lalle abubuwa da yawa sun faru da banji dadinsu ba, balanta na yadda aka watsar da yan wasan. Amma komai ya wuce tunda kwantaragi na ya kare. Abinda ya rage shine hakkina kuma shine yafi amfani.

Saidai ministan matasa da wasanni, ya roki NFF su biya Siasia. Dalung ya bayyana haka lokacin da yakarbi bakoncin Siasia da matar sa Eunice da Muhammad Sanusi sakataren NFF a ofishin shi dake Abuja ranar litinin 29, Agusta.

Ministan ya umurci sanusi da su tabbata sun biya Siasia hakkokan shi na watanni 5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel