Yan siyasa ke daukan nauyin makiyaya dake kai hare hare – Jigon APC

Yan siyasa ke daukan nauyin makiyaya dake kai hare hare – Jigon APC

Mataimakin shugaban jam’iyar APC a yankin kudancin Najeriya Cif Segun Oni ya zargi yan siyasa da hannu cikin haren haren da ake kai ma al’ummomi da dama a kasar nan wanda ake zargin makiyaya da aikatawa.

Yan siyasa ke daukan nauyin makiyaya dake kai hare hare – Jigon APC

Oni yayi wannan zargin ne a wata hira da yayi da sakatariyar jam’iyar dake Abuja a ranarv 30 ga watan agusta, yace nufin yan siyasan shine su hargitsa kasar tare da gwamnatin tarayya. Yace “wannan lamarin na damuna saboda mutanen dake hare haren nan ba baki bane, sun dade ana tare dasu. Ina tunanin wasu ne ke daukan nauyinsu don cin ma wata manufar su”

“ina da yakinin yan siyasa ne ke daukan nauyinsu don su kawo tarnaki ga gwamnati mai ci. Mutanen da basu son zaman lafiya ne ke shirya wannan abin. Abin nada wuyar ganewa, zaka ji labarai daban daban kan batun, hakan na nufin ba karamin abu bane wannan.”

Jigon jam’iyar APC yace gwamnati ta cirri tuta wajen magance matsalar tsaro, amma yace ya kamata a kara dagewa. Kazalika a jiya ne Segun Oni ya roki yan Najeriya da su kara hakuri da shugaba Buhari a kokarin da yake yi na daidaita kasar nan.

Oni yace ba laifi bane jama’a su sa ran Buhari zai gyara kasar nan da gaggawa, sakamakon halin da kasar ta tsinci kanta a baya. Amma ya ja hankalin yan Najeriya cewa babu wani tsafin da zai fitar da kasar nan daga halin lalacewar tattalin arziki.

Oni ya kara da cewa jam’iyar APC zata yi iya kokarinta wajen kawo ma kasar nan cigaba, ya ce idan da ace PDP ne akan karagar mulki, toh da halin tattalin arzikin ya munana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng