Tsoffin ma’aurata masu sanya tufafi iri daya kullum
Soyayya gamon jinni, inji masu iya magana, sa’annan a kulli yau min ana samun karuwar fahimtar tsananin soyayya a tsakanin ma’aurata.
Hotunan wasu ma’aurata da suka shafe shekaru 52 suna tare a zaman aure ya yadu sosai a shafin yanar gizo.
Jikanyar ma’auratan Anthony Garguila ne ya daura hotunan kakannin nasa a kafar sadarwa ta twitter inda yayi ma hotunan taken “yau shekarun kakannina 52 suna tare, kuma suna sanya tufafi iri daya a kullum.”
A gaskiya hotunan sun nuna tsanani da karfin soyayya dake tsakanin ma’auratan, wannan ya nuna cewa suna tsananin shaukin juna, tare da fahimtar juna, hakan ya sanya suka birge duk wanda ya kalli hoton.
Wannan shi ne kwatan kwacin soyayyar da ya kamata mutane su nuna ma junansu, sa’annan shi ne misalin soyayyar gaskiya.
Asali: Legit.ng