Anyi ‘Operation Crocodile smile’ don gogar da manyan jami’an soja ne- Rundunar Soja

Anyi ‘Operation Crocodile smile’ don gogar da manyan jami’an soja ne- Rundunar Soja

Rundunar sojan kasarnan tayi bayani dangane da aiki na musamman data kaddamar a yankin Neja Delta mai taken ‘Operation Crocodile Smile’ wato samamen dariyar kada, a cewar rundunar, aikin ba yana nufin kai hare hare ga tsagerun neja delta bane.

Akwai rahotanni da dama dake nuna cewa an kaddamar da aikin ne domin yakar yan ta’addan yankin Neja Delta. Sai dai jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun hukumar Sojan kasarnan Birgediya janar Rabe Abubakar yana cewa aikin na musamman ba shi da alaka da kai ma tsagerun Neja Delta hari.

Anyi ‘Operation Crocodile smile’ don gogar da manyan jami’an soja ne- Rundunar Soja
Birgediya Rabe Abubakar

Rabe Abubakar ya bayyana cewa an shirya aikin ne a matsayin atisaye na musmman da zai gogar da jami’an sojan kasa. Amma fa yace idan tsagerun suka taba wani soja daga cikin su a yayin atisayen, toh tabbas sojoji zasu kare kansu.

Yace “ya kamata a fahimci manufar wannan aikin da muka fara a Neja Delta, ba don tsagrun Neja Delta muka shirya shi ba. Mun shirya shi ne a matsayin atisaye da zai gogar da jami’an sojan kasa dangane da aiki akan ruwa. Atisaye ne kawai, toh a lokacin da suke farfasa bututun mai kunga sojoji a yankin ne? “amma fa idan muka fahimci wata barazana daga tsagerun, toh ya zama wajibi mu kare kanmu. Atisayen na tafiya yadda ya kamata zuwa yanzu, bamu da shirin kai ma kowa hari sakamakon maganan sulhu da ake yi. Fatar mu shi ne a zauna lafiya.

Wannan aiki na musamman da rundunar soja ta kaddamar a yankin Neja Delta ya sanya wata kungiyar tsagerun Neja Delta mayar da martani, inda wata kungiya mai suna Niger Delta Greenland Justice Movement (NDGJM) ta fasa wani bututun mai dake Ogor-Oteri mallakan hukumar kulawa da cigaban man fetur.

Shugaban kungiyar tsagerun Janar Aldo Agbalaja ya bayyana cewa sun fasa bututun man ne da misalin karfe 3 na daren talata 30 ga watan agusta, inji jaridar Vanguard. A cewarsa, zasu kaddamar da aikin su kishiyar na sojoji “Operation Crocodile Smile” wato ‘samamen murmushin kada’ don su kara rura wutar tashin tashinan da ake fama da shi a yankin Neja Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel