Kalli abinda wani dalibi matashi ya kirkiro a Kenya

Kalli abinda wani dalibi matashi ya kirkiro a Kenya

Duniya zata amfana idan zamu yi aiki da fasahar da yara matasa ke da ita na kirkiro abubuwa

Akwai mutane da yawa masu basira da fasaha a cikin al'umma; matasa a cikinsu na amfani da lokacinsu wajen yin abubuwa masu amfani kuma basu yarda su afka cikin aikin ashsha ba, mamadin haka sun gwammace suyi amfani da rayuwarsu wajen gyara zamantakewarsu.

Kalli abinda wani dalibi matashi ya kirkiro a Kenya

Wannan labarin wani dalibin jami'ar Nairobi ne mai suna Arnold Bett, wanda mai bincike ne kan harkokin naurori masu aiki da wutar lantarki. Wannan dalibi yayi abin azo a gani yayin da ya kirkiro jirgin sama mai tuka kansa

Bett, wanda dan kasar Kenya ne, ya gano bukatar dake akwai na kirkiro wannan jirgin domin taimakama binciken aikin gona. Wannan abu ne mai alfanu in akayi la'akari cewa noma na da muhimmanci kan tattalin arziki

Dalibin matashi, ya kirkiro jirgin maras matuki koko Unmanned Aerial Vehicle (UAV) a turance wanda ke aiki da baturorin da ake gasawa. Yana da nauyin 2.5kg, kuma zai iya daukar na'urar daukar hoto dana  aune-aune ya kuma tashi tsawon mita dari biyu. An yi gwajin wannan nau'ura mai kyau wajen samun bayanai kan noman dankali a kasar Tanzania. An bayyana wannan hanya ta tattara bayanai a matsayin ci gaba domin yawan bayanan da ake iya samu da kashe kudin kalilan. Masu bincike sunce ana iya duba manyan ayyuka ba tare da amfani da tauraron dan adam ba. Na'urar zata taimaka wajen taswirar noman rani inda za'a gane wuraren da ruwa bai isa ba. UAV din ya taimaka wajen gano iri goma sha hudu na dankali a Tanzania.

KU KARANTA : CAN ta maida martani kan kisan Kiristoci

Arnold Bett ya nuna fasaharsa a wani bukin baje koli da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta, ya halarta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng