Matasan PDP sun bukaci Buruji Kashamu ya koma APC
-Matasan PDP sun gaya ma sanata Buruji Kashamu ya fito fili yace dan APC ne mamadin yaudara cewa dan PDP ne
-Matasan sun ce Mallam Nasir El-Rufai da Ministan sufuri Mr Rotimi Amaechi na amfani dashi domin lalata PDP
Matasan PDP sun bukaci sanata mai wakiltar Ogun ta gabas Buruji Kashamu da ya fito karara yace shi dan APC ne mamadin yaudarar da yake cewa shi dan PDP ne. Matasan na wata kungiyar matasan PDP (PDPYC) sunce Sanata Buruji Kashamu yafi kusa da dan APC kuma ya kamata yaje ya shiga APC mamadin yana Kiran kanshi dan PDP amma kuma yana kare gwamnatin APC.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar Mr. Oluwole Durojaiye, ya bayar wadda ke cewa ya kamata duk masoya PDP a kudu maso yamma su gane cewa sanata Kashamu dan leken asirin APC ne, kuma zai iya yin duk abinda zai lalata PDP. PDPYC tana cewa sanata kashamu na aikin kakakin APC kuma zai yi kyau matsayin canjin Lai Mohammed a matsayin sakataren watsa labarai na APC domin yana aikin kare duk matakan da gwamnatin tarayya ke dauka wadanda ke ma damokradiyya karan tsaye fiye da wanda masu magana da yawun shugaban kasa ke yi.
KU KARANTA : Majalisar Amintattun PDP sun mayar da taro Abuja
Sun zargi Kashamu da kashe fiye da N100m domin wallafa batanci game 'yan PDP, amma bai kashe ko kobo ba domin buga abin batanci game da gwamnatin APC ba. Sun kuma zargeshi da kashe fiye da N2b domin samun hukunce hukuncen kotuna marasa kyau ga PDP. Kungiyar tace mafarin faduwar zabe da Jam'iyyar tayi ya samo asali daga hukuncin kotu da Kashamu ya samo wanda ya sauke Olagunsoye Oyinlola, Chief Bode Mustapha da Chief Segun Oni daga mukamansu. Suka ce, yayin da yake wannan, gwamnan jihar Ogun na bashi kwangiloli, daya daga ciki shine na sawo ma majalisar walkilai ta jihar motochi
Asali: Legit.ng