An yi ma wata mata dukan tsiya a Coci
A kasar Kenya wata mata mai suna Halleluya Amta ta bayyana cewa anyi mata dukan tsiya a coci su mai suna Catholic church,kwale County saboda ta sa kaya mara kyau.
Game da cewar jaridan Standard, Amta ta bayyana cewa wadanda su ka ci mata mutuncin ma’aikatan cocin ne maza 2 da mace 1 a Saint Joseph, Ukunda Catholic church tace : “Na zo coci ne da wannan tufafin amma aka ture ni,aka zage ni ,aka doke ni.”
Amta ta ce ta sanya bakin wando matsatse amma ta rufe da dogon kaya kuma tana rike da jakanta da leman ta. Abin mamaki,sai aka hanata shigab coci inda suke cewa bata sanya kaya masu kyau ba. Amta tace ta yar da kudi Sh 50, 000 a hayaniyar kuma ta kai kara. Kana kawarta Nimos Baraza tace a gaban ta abin ya faru.
KU KARANTA : Wani fasto yayi luwadi da dan shekara 13
Baraza tace : “Na raka ta cocin ne. sun kusa kada ta. Nace mata mu koma saboda rain a y abaci. Wasu tsofaffi ne wadanda suka mayar da kansu masu gadi ,ban tunanin ma arna ne.”
Asali: Legit.ng