Wani fasto yace yana da ikon kashe kowaye

Wani fasto yace yana da ikon kashe kowaye

Wani majanuni, fasti a kasar Zimbabwe ya ce ubangijinsa ya bashi karfin kashe duk wanda yaga dama.

Faston mai suna Emmanuel Makandiwa,yayi ikirarin cewa yan da karfin ikon kashewa. Ya fadi dukkan wannan ne a wata jawabi da ya gabatar a aron tsakar dare da akayi a mount Hampden a ranan juma’an da ya gabata.

Wani fasto yace yana da ikon kashe kowaye

“ Ranar yin hukuncin nmu yaki ne kuma mun zo nan domin aika duk wani shaidani . fastoci na kashe mutane hakazalika ni ma ina da karfin kashe duk wanda zai zaman mini cikas a aikin da ubangijina ya turo ni. Idan aka kama yan baranda ai kurkuku ake kaisu saboda mutane su samu sukuni. Saboda haka munzo nan ne domin mu tura duk kalubalen rayuwan mu kurkuku domin mu samu zaman lafiya. Afrika na da arziki amma turawa sun sanya ma arzikin mu ido. Shi yasa lokacin da masu yada addinin kirista suk zo yadawa, suna son mu mutu ne saboda su ci gado arzikin da Ubangiji ya bamu.

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel