Wasu ma'aurata yan Najeriya sunyi auren kece raini
Wasu ma'aurata kiristoci, sun kama hannu zuwa ibadar aure.
Soyayya abu mai kyau ne, Adefunke da Adebola sunyi auren soyayya alokacin da suka kama hannu, suka sa sutura mai kalar jinin kare dakuma ruwan zinare hade da murjani a bikin auren auresu na al'ada.
Ma'auratan kiristocin sunyi bikin auren su tare da yan uwa da abokan arziki. Amfara shagalin lokacin da amarya ta shuga taron tana mai dauke hankalin jama'a, kiristan da ake bege wanda kuma akafi sani d Myss Lafunki, yanada shafinsa a yanar gizo wanda yake taimakama kiristoci akan zamantakewa, inganta soyayyar uban giji dakuma ilmantar da mutane akan tsarkakken jima'i.
A al'adar yar Bawa, bayan an kaima amarya kayan aurenta anaso kuma ango ya roki amaryarsa kozata aureshi. Hakan ke hukunta cewar an daura aure kuma ma'auratan sun zama daya.
Asali: Legit.ng