Shugaban kasar North Korea ya bada umurnin kashe wasu jami'an gwamnati
–Shugaban kasar North Korea Kim Jong-un,ya bada umurnin kisan wasu jami'an gwamnati guda 2
–An kasha jami'an ne ta hanyar bindige su
–An kashe daya domin yana bacci lokacin ganawa da shugaban, dayan kuma domin fito na fito da shugaban
Shugaban kasar North Korea Kim Jong-un,ya basa umurnin hallaka wasu ma'aikatan gwamnati domin saba masa.
Jaridar JoongAng Ilbo ta bada rahoton cewa tsohon ministan aikin noma Hwang Min da babban ma'aikaci a ma'aikatar ilimi Ri Yong jin ,ne aka kashe. Wata majiya tace an kashe Ri Yong Jin ne bayan ya kasance yana gyangyadi lokacin wata ganawa da shugaba Kim.
“Aka tsare shi kuma ska yi masa tambayoyi. An kashe shi ne akan laifuffuka irinsu rashawa da aka same sa da shi. Na gane cewan an kashe shi ne saboda wasu abubuwa da ya gabatar mai kalubalantar shugabancin Kim Jong-Un.”
Ana bada rahoton cewa an kashe su ne a makarantan horon sojoji da ke babban birnin kasar Pyongyang, a farkon wannan watan.
KU KARANTA : An ba da kwangilar $1.85 Biliyan na jirgin kasa a Kano
Kim ya hau karagar mulki ne a shekarar 2011 bayan mutuwar mahaifin sa Kin jong II, kuma ya kasha manya da dama a gwamnatin sa. Wani dan oekan asirin South korea yace a shekarar da ya gabata, an kasha wani tsohon ministan tsaro Hyun Yong Chol, Da laifin yaudarar kasa.
Asali: Legit.ng