kwaliyar mai da tsohuwa yarinya a cuci maza ko burgewa
1 - tsawon mintuna
Kwalliyar da aka saba ita ce ta sanyan dan jan baki da ‘yar hoda, amma yanzu abin ya wuce haka sakamakon bullar wasu masu sana’ar kwalliyar mai da tsohuwa yarinya.
Wata mai kwalliya ta nuna kwarewarta a wannan fanni, a yayin da ta shekawa wasu zabiya kwalliya ta ban mamaki, domin ta yi nasarar batar da kamanninsu gaba daya zuwa wata kyawawa.
Shin irin wannan kwalliya kasaita ce, ko kuwa a cuci maza ne a yayin da aka mayar tsohuwa yarinya? Gani dai ya kori ji.
Wannan salon kwalliya ta janyo ka-ce-na-ce a dandalin sada zumunta da muhawara na Intanet, yayin da wasu ke ganin cewa irin wannan kwalliya a cuci maza ne, wasu kuma na cewa burgewa ne, shin ko menene ra'ayinku ku?
Asali: Legit.ng