Mace ta farko take tuka jirgin sama

Mace ta farko take tuka jirgin sama

a shekarun baya ne aka samu mace kuma bakar fata ta farko data fara tuka jirgin sama a kasar Afirka ta Kudu. Ku saurari labarinta.

Ita dai wannan budurwar sunan ta Asnath Mahapa yar asalin kasar Afirka ta kudu, kuam ta zamanto mace ta farko daga cikin bakaken fata data fara sarrafa jirgin sama a kasar. Wannan ya kasance tamkar wata nasara ce ga yaya mata da kuma yaki da nuna wariya tsakanin maza da mata a kasar. Sai dai Asnath ta bayyana cewa nasarar bata zo mata cikin sauki ba.

A lokacin da take karama ta kan zura ido tana mamakin yadda jirgi ke tashi a sama, da haka ne ta fahimci lallai duk kankantan mutum zai iya sarrafa jirgin sama duk girmansa. Daga nan ne fat a fara sha’awar karantar yadda ake tuka jirgi, kuma ta dage da kokarin wajen ganin ta zamto matukiyar jirgi, duk da irin tsangwamar da ake nuna ma mata a kasar, musamman ma bakaken fata.

Mace ta farko take tuka jirgin sama

Asnath ta cire kanta daga makarantar da take zuwa kuma ta shiga daukan darasi kan tukin jirgin sama ba tare da goyon bayan mahaifinta ba. Ita kadai ce mace a ajin, don haka ta zamto mai kwazo wajen ganin ta cika burinta. A lokuta da dama idan tana tuka jirgin sai ta dinga jin zazzabi, amma duk da wannan bata fasa karatun ba.

A shekarar 1998 ne Asnath ta kasance mace ta farko bakar fata data fara tuka jirgi a kasar Afirka ta kudu lokacin tana da shekaru 22, sa’annan bayan shekaru 14 ta bude makarantar koyon tuka jirgin sama na mata zalla, saboda ta samu isashshen kwarewa na gogar da yan mata masu irin ra’ayinta.

Mace ta farko take tuka jirgin sama

Ga abinda tace: “Ya zama dole maza su yarda cewa mata na iya zama duk abinda suke so, kuma sun mata dole ne su yarda cewa zasu iya zama duk abinda suke so, zancen hana bambanta jinsi ba a baki bane kawai, dole ne ta dage wajen aikata zancen, a haka ne zata cika burinta, kuma ta kara ma yan baya kwarin gwiwa.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng