Jami'ar Afe Babalola sun hana dalibai amfani da wayar salula masu hikima.
Jami'ar kudu dake Najeriya, sun zantar da dokar hana dalibansu amfani da wayar salula wacce ake shiga yanar gizo da ita a harabar makarantar.
A wani sabon ci gaba, daliban daya daga cikin jami'um kudi masu daraja a Najeriya, wato jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti [ABUAD], mahukuntar sun bada umarnin da a daina amfani da wayar hannu da za'a Iya shiga yanar gizo da ita dama sauran wasu nau'ikan kalan wayoyin irin su tablets.
Dokar wadda ta shafi tsofaffin da sababbin dalibai na makarantar, amman saidai basuyi maraba da ita wannan sabuwar dokar ba, domin kuwa sun nuna a fili basu boye ba, musamman masu amfani da kafaffen yada labarai na yanar gizo.
Gadai abunda hukumar makarantar tace dangane da fitar da dokar, " wayar tafida gidanka, jami'ar ta yarda da amfani da waya amman wa'anda ba'a Iya shiga yanar gizo dasu, duk wayar da jami'ar bata amince da itaba, harda tablet ko IPad to za'a anshe ta kuma daga baya a hukunta dalibi.
Asali: Legit.ng