Karkar Nigeria ta yanke saka da samun ma'adinai a Kaduna

Karkar Nigeria ta yanke saka da samun ma'adinai a Kaduna

-Wani kamfani taki sa a a Kaduna

-Kamfanin ya hako wani ma’adini mai daraja a duniya

-Ma’dinin ka iya sauya matsayin Najeriya a duniya

Karkar Nigeria ta yanke saka da samun ma'adinai a  Kaduna
Dakta Kayode Fayemi, Ministan kula da albarkatun kasa da ma'adinai

Kafar yada labarai ta Premium Times ta bayar da rahoton cewa, Nigeria ta yi babban gamo na alheri da gano wani ma’adini mai matukar daraja, a arewacin kasar.

Rahoton wanda kafar yada labaran ta wallafa a shafinta na intanet, a ranar Litinin 29 ga watan Agusta na cewa, wani kamfanin Kasar Australia ne ya ba jaridar kasar labarin cewa, wasu masu hakar ma’adinai da ba na gwamnati ba, karkashin shugabancin Hugh Morgan ne ya hako ma’adinin a kauyen Dangoma da ke arewa maso yammacin jihar Kaduna.

A cewar rahoton, kamfanin na cewa, “binciken ya gano samun wannan dutsi mai matukar daraja a kasa, wanda hakan ke nuna cewa, idan aka yi haka mai nisa za’a taras da babban dutse mai girman gaske na wannan ma’adini.”

Kafar yada labaran ta ambato Kamfanin Morgan na cewa, sun yi tsammanin gwamantin Najeriya za ta sanar da wannan babban alheri a hukumance, amma rahoton ya ci gaba da cewa, babban jami’in hulda da ‘yan jaridu na Ministan Ma’aikatar kula da albarkatun kasa Mista Olabode Olayinka, ya ce ba shi da labarin wannnan al’amari.

Sai dai ya tabbatar da cewa Ministan Ma’aikatar, Kayode Fayemi zai je kasar Australia a mako mai zuwa, a inda zai yi jawabi a wani babban taro na kwanaki uku kan harkar ma’adinai a Africa, wanda za a yi otal din Perth Pacific a Australia amma bai san ko a kan me Ministan zai yi jawabi ba.

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel