Ma'aikacin filin jirgin sama yayi mumunan mutuwa

Ma'aikacin filin jirgin sama yayi mumunan mutuwa

–Wani ma'aikacin filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Jihar Legas ya mutu a dakin mazinaciya

–Mutumin mai suna Sikiru Olanrenwaju yanada aure da yara amma yana bin yan matan banza

–Ya mutu ne a cikin dakin wata mata da aka sakaye sunanta.

Ma'aikacin filin jirgin sama yayi mumunan mutuwa

Sikiru Olarenwaju ma'aikaci ne na wata kamfani a babban filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Ikeja. ya bar Gida ne ranan talata ,23 ga watan agusta domin zina da wata mata, sai yayi karo da ajalinsa.

Game da cewar ofishin yan sandan Jihar Legas, ya rasu ne a titin surulere da ke Abule Egba,a Legas. Kakakin ofishin yan sandan , Dolapo Badmos, ta tabbatar da labarin ga manema labarai cewa:

“Wata tawagar yan sanda daga Oke-odi sun je inda abin ua faru . mun samu cewan babu wani alaman ciwo a jikin mamacin. An kai gawar wajen ajiye gawawwaki. Amma ana gudanar da bincike.

Game da cewar Jaridan Punch, lokacin da mamacin ya zo gidan matan, sunci abinci tare da ita matar. Sai suka yi jima'i. Misalin karfe 5 na safe, ta tashe shi ya tafi wajen aiki amma sai ta gano babu rai a jikin shi. Da wuri sai tayi kira ga makwabta har da maigidan Wadanda suka kai kara ofishin yan sanda.

KU KARANTA : Karanta yadda akayi garkuwa dan shekara 2 a Jihar Legas

A bangare guda, asibitin jihar ogun ta tabbatar da mutuwan wata mata mai suna Gbemisola Edward,da yar ta Dolapo, sanadiyar kunan wuta. Game da cewar Jaridar punch, mijin Gbemisola Edward, ya watsa musu man fetur ne ya banka musu wuta. Yaran da ya tsira ya ce mijin ya ce ma matar ta sayar da gidansu amma ta kiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel